in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kafa kawancen farfado da tambura don raya kasa a Beijing a yau
2019-05-10 14:35:33 cri

Yau Jumma'a ranar 10 ga wata, aka kafa kawancen farfado da tambura don raya kasa a birnin Beijing, hedkwatar mulkin kasar Sin, wanda ya kunshi mambobi fiye da 1000.

Wannan kawancen da babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin na CMG ya gabatar ya kunshi mambobi kimani 1200 da suka shafi hukumomin gwamnatin tsakiya, gwamnatocin wurare, shahararrun kamfanoni, jami'o'i da kwalejoji, hukumomin nazarin kimiyya, kungiyoyin kula da harkokin sana''o'i, da ma kwararru a fannoni daban daban. A cikin sanarwar hadin gwiwa da mambobin suka bayar, an ce, kawancen zai hada kansu da ma sassa daban daban na zaman al'umma sosai waje yada amfanin tambari yayin da ake kyautata ayyukan raya kamfanoni, domin biyan bukatun jama'a na jin dadin zaman rayuwa.

A yayin bikin kafa kawancen kuma, Shen Haixiong, shugaban CMG ya furta cewa, a halin yanzu, kamfanonin da ke da shahararrun tambura wadanda yawansu ya kai kashi 20 cikin dari, yawan kayayyakin da suka samar ya kai kaso 80 na duk duniya. Lallai akwai babban gibi a tsakanin kamfanonin Sin da wadanda suka shahara a duniya. Don haka ya kamata a gaggauta aiwatar da manufar farfado da tambura domin kyautata tamburan kasar Sin har su kai matsayin farko a duniya, ganin yadda suke da babban karfin sirrin ci gaba.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China