Jiya Lahadi a nan Beijing aka bude bikin baje-kolin fasahar yada labarai na duniya dangane da kirkire-kirkire kan yada labarai bisa fasahar 5G+4K.
Wakilai daga kafofin yada labaru da hukumar tsara hoton bidiyo na kasashe da yankuna wadanda suke cikin shawarar "ziri daya da hanya daya" sun gwada fasahar zamani da kuma sabbin na'urorin daukar bidiyo a wurin nune-nunen fasahar yada labarai ta zamani.
Bikin da babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin na CMG da kawancen hadin kai na duniya na hanyar siliki da shahararrun kamfanonin na'urorin kasa da kasa suka shirya, ya kasance a matsayin wani dandalin nune-nunen fasahar zamani da yin hadin gwiwa da mu'amala a tsakanin kafofin yada labaru na kasa da kasa.
Tun bayan kafa hukumar shekara guda da ta gabata, CMG tana tsayawa kan yin krikire-kirkire da yin jagora, ya kama zarafin fasahar 5G. Ya kafa dandali na farko na yada labarai ta sabbin hanyoyi bisa fasahar 5G a kasar Sin. Wannan shi ne karo na farko da ya tsara tare da daukar bidiyo bisa fasahar 4K da kuma yada bayanai bisa fasahar 5G. (Tasallah Yuan)