in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
CMG ya kaddamar da gidan gwajin fasahar sadarwa ta 5G+4K+AI a birnin Shanghai
2019-05-05 16:47:24 cri

 

Babban gidan rediyo da talabijin na kasar Sin(CMG) a yau Lahadi ya kaddamar da gidan gwajin fasahar sadarwa ta zamani ta 5G+4K+AI a birnin Shanghai na gabashin kasar Sin, bikin da ya kuma alamanta fara aikin daukar shirin bidiyo mai taken "cikar yankin Pudong shekaru 30". Mataimakin shugaban sashen fadakar da jama'a na kwamitin kolin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana shugaban gidan CMG, Mr.Shen Haixiong, da mataimakin sakataren kwamitin kula da harkokin Shanghai na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, wanda kuma shi ne magajin garin birnin na Shanghai, Mr.Ying Yong, sun halarci bikin.

A yayin bikin, Mr.Shen Haixiong ya yi nuni da cewa, a cikin shekara guda da kafuwar CMG, an mai da hankali sosai a kan bunkasa fasahar zamani ta 5G+4K+AI, fasahar da aka kuma yi amfani da ita a wasu manyan rahotannin da ya bayar, wanda kuma ya haifar da babban tasiri. (Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China