in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
CMG da kungiyar kwallon kafa ta Italiya sun daddale takardar hadin kai ta fuskar watsa shirin gasannin kwallon kafa na Italiya
2019-03-25 09:19:03 cri

Jiya Lahadi ranar 24 ga wata, babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin na CMG da kungiyar kwallon kafa ta kasar Italiya sun cimma yarjejeniyar hadin kai daga dukkan fannoni, lamarin da ya sa ake sa ran za a rika kallon gasannin kwallon kafan kasar Italiya wato seria A, a kasar Sin a cikin shekaru uku masu zuwa.

An daddale wannan takardar bayanin ne domin aiwatar matsayi daya da shugabannin kasashn Sin da Italiya suka cimma wajen zurfafa amincewar juna da hadin gwiwa a fannoni daban daban, da ma kara bunkasa sha'anin kwallon kafa na kasashen biyu da yadda za a watsa shirye-shiryen da ke da nasaba da wasannin kwallon kafa.

A yayin bikin daddale takardar, shugaban CMG, Shen Haixiong, ya bayyana cewa, babu shakka hadin gwiwar bangarorin biyu a fannin kwallon kafa zai bude wani sabon babi na cudanyar kasashen biyu a fannin wasanni da al'adu. Ya kuma furta cewa, CMG zai yi iyakacin kokarinsa wajen mara wa sha'anin kwallon kafa na kasar Sin baya a fannin hadin kai tare da Italiya, ta yadda za a kara bunkasa dangantakar da ke tsakanin Sin da Italiya.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China