Shugaban sashen fadakar da jama'a na kwamitin koli na JKS Huang Kunming ya yi kira da a kara mai da hankali kan kirkire-kirkiren fasahar kere-kere da kara cin gajiyar sabbin kafofin watsa labarai a kokarin kasar na bunkasa kafofin watsa labarai.
Huang Kunming ya yi wannan kiran ne ranar Talata, lokacin da ya ziyarci dakin binciken fasahar 5G da babban rukunin kafofin watsa labarai na kasar Sin CMG ya kafa, wadda aka kaddamar a shekarar da ta gabata bayan hade babban tashar talabijin ta CCTV da rediyon kasar Sin da gidan rediyon CRI.
Ya bukaci babban rukunin na CMG da ya tabbatar da cewa, ya tantance dukkan kayayyakinsu da ke da nasaba da fasahar 5G, ba wata tangarda, sannan za su biya bukatun jama'a a fannin ingancin shirye-shiryen talabijin da hotuna masu inganci.(Ibrahim)