in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilin musamman na kasar Sin kan harkokin Afirka ya ziyarci Sudan
2019-05-10 11:15:37 cri

Xu Jinghu, wakilin musamman na kasar Sin mai kula da harkokin Afirka, ya ziyarci kasar Sudan daga ranar 3 zuwa 7 ga wata, inda ya gana da shugaban kwamitin mulkin soja na wucin gadi Abdel-Fattah Al-Burhan da mataimakinsa Hossein Hamadani da mukaddashin ministan harkokin wajen kasar Faisal Hassan Ibrahimm, daya bayan daya.

Xu Jinghu ya ce, kasar Sin za ta ci gaba da mara wa jama'ar Sudan baya da su zabi hanyar raya kasarsu bisa halin da suke ciki. Kuma Sin na fatan sassa daban daban na Sudan za su cimma daidaito ta hanyar tattaunawa, za kuma su gudanar da shirin shimfida wani tsarin siyasa na wucin gadi, a kokarin tabbatar da zaman lafiya, kwanciyar hankali da ci gaba a kasar. Ya ce duk sauye-sauyen da za a samu, ba za su raunana dankon zumuncin da ke tsakanin Sin da Sudan ba, kana kasashen 2 ba za su canza manyan tsare-tsaren raya hadin gwiwa da abota a tsakaninsu ba.

Bangaren Sudan ya nuna cewa, kullum Sin na mara masa baya. Kuma an samu sakamako mai kyau karkashin hadin gwiwar kasashen 2. Ya ce Sudan za ta ci gaba da himmantuwa wajen raya hadin gwiwa a tsakaninta da Sin bisa manyan tsare-tsare, a kokarin bunkasa huldar da ke tsakanin kasashen 2 zuwa gaba. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China