Sanarwar wadda Shams-Eddin Kabashi, kakakin majalisar TMC ya fitar a lokacin taron manema labaru a Khartoum.
Ya ce TMC ta mika rubutaccen martani game da daftarin dokar kundin tsarin mulkin kasar wanda kungiyoyin adawa na Freedom da Change Alliance suka gabatar tun da farko.
Ya kara da cewa, TMC ta adana wasu muhimman bayanai a cikin daftarin, yayin da take duba yiwuwar cimma yarjejeniya kan wadannan bayanan da ta adana.
Sai dai ya ce daftarin bayanan bai kunshi batun majalisar dokoki ba, da wa'adin da za'a kwashe kafin mika mulki, da kuma karfin ikon da majalisar mulkin da za'a kafa take da shi. (Ahmad Fagam)