in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mukaddashin babban mai gabatar da kara na Sudan ya kirawo tsohon shugaba al-Bashir
2019-05-03 16:03:48 cri

Ma'aikatar shari'a ta kasar Sudan, ta ba da wata sanarwa a ranar 2 ga wata cewa, a wannan rana mukaddashin babban mai gabatar da kara na Sudan, ya ba da umurnin kirawo tsohon shugaba Omar al-Bashir.

Sanarwar ta ce, mukaddashin babban mai gabatar da kara ya ba wannan umurni ne bisa dokokin da suka shafi cinikin musayar kudi, da kuma yaki da halasta kudin haram, da ba da tallafin kudi ga 'yan ta'adda. Sa'an nan kuma ya ba da umurnin bin bahasin wasu jami'ai da suka taba aiki a gwamnatin al-Bashir, dangane da huldar su da hada-hadar kudi.

A ranar 1 ga watan Mayu, bangaren masu gabatar da kara na Sudan, ya umurci a kwace dukiyoyin wasu manyan jami'an da suka taba aiki a gwamnatin al-Bashir.

A ranar 11 ga watan Afrilun bana, ministan tsaron kasar Awad Mohamed Ahmed Ibn Auf, ya sanar da hambarar da gwamnatin al-Bashir, tare da kafa kwamitin soja na wucin gadi mai mulkin kasar. Kashe gari kuma, Awad Mohamed Ahmed Ibn Auf ya yi murabus daga mukaninsa, na shugabancin kwamitin soja na wucin gadi.

A ranar 14 ga watan jiya, ma'aikatar harkokin wajen Sudan ta ce, kwamitin soja na wucin gadi zai aza harsashin kafa gwamnatin fararen hula don mulkin kasar, kuma zai mika musu mulkin kasar cikin shekaru 2 masu zuwa. (Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China