"Har zuwa wannan lokacin, ba mu samu wasu rubutattun bayanai daga tawagogin masu shiga tsakani ba kuma ba mu yi wata tattaunawa game da batun yin wakilci a majalisar shugabancin kasar ba," Shams-Eddin Kabashi, kakakin majalisar ta TMC, shi ne ya bayyana hakan a taron manema labarai.
Ya kara da cewa, TMC tana sa ran za ta kammala yin nazari kan bayanan da kungiyoyin 'yan hamayya suka gabatar, yana mai cewa ana sa ran za'a karbi martanin da TMC ta gabatar a ranar Litinin.
Ya kuma bayyana kyakkyawar fatar samun nasara a tattaunawar mika shugabancin kasar da ake gudanarwa, yana mai cewa, "babu wata babbar matsalar dake kawo cikas, kuma muna da kyakkyawan yakinin za mu samu nasarar cimma matsayar warware matsalar cikin hanzari a bisa irin cigaban da muka samu a tsakanin bangarorin biyu." (Ahmad Fagam)