in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin MDD sun bukaci a dauki matakan magance matsalar sauyin yanayi
2019-05-10 10:04:02 cri

Babban sakataren MDD Antonio Guterres ya jagoranci bude taron wuni biyu na manyan jami'an MDD a ranar Alhamis, inda a lokacin taron shugabannin hukumomin MDDr sun bayyana wasu himman matakai da ya kamata a dauka don shawo kan matsalar sauyin yanayin gabanin babban taron kolin MDD kan sauyin yanayi wanda zai gudana.

A wata sanarwa mai taken "Kiran hadin gwiwa daga tsarin MDD zuwa ga babban sakatare a taron koli game da sauyin yanayi", shugabannin hukumomin MDDr sun ce a shirye suke su kara karfin hukumominsu domin kai dauki ga bukatar mambobin kasashen dake da bukatar rage tasirin da sauyin yanayi ke haifarwa.

"Samar da kudaden yaki da sauyin yanayi wani muhimmin mataki ne wajen shawo kan matsalar sauyin yanayi," jami'an MDD sun bayyana cikin wata sanarwa, inda suka bukaci kasashen da suka ci gaba da su dukufa wajen wayar da kan gwamnatoci da bangarori masu zaman kansu da su tabbatar da cimma burin samar da dala biliyan 100 a kowace shekara ya zuwa shekarar 2020 don tallafawa shirin yaki da sauyin yanayi a kasashe masu tasowa kuma su kara rubanya kokarinsu wajen tattara kudaden da ake bukata wajen aiwatar da shirin. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China