A cewar tawagar kasar Sin, ko da yake kason kudin da kasar Sin ke bayarwa ya karu sosai, amma kasar ta biya dukkan kudaden da ake bukata a shekarar 2019 cikin lokaci, ba tare da gindaya wani sharadi ba. Hakan ya nuna cewa, kasar Sin babbar kasar ce mai tasowa dake daukar nauyin da aka dora mata, wadda kuma ke goyon bayan MDD a harkokinta daban daban, musamman ma kan tsarin kasancewar bangarori daban daban a duniya. Wannan matakin da kasar Sin ta dauka ya sa ta samu yabo daga daukacin mambobin MDD, gami da sakatariyar majalisar. (Bello Wang)