in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Masar ya ce kamfanonin fararen hula ne ke aiwatar da ayyukan raya kasa ba sojoji ba
2019-05-06 14:01:06 cri
Shugaban Masar Abdel-Fattah al-Sisi, ya ce dukkan kamfanonin dake ayyukan raya kasa a kasar na fararen hula ne, ya na mai jaddada cewa, rawar da sojoji ke takawa a ciki ita ce sa ido.

Abdel-Fattah al-Sisi ya bayyana jiya, yayin kaddamar da wasu jerin ayyukan raya kasa a birnin Ismailia dake kusa da mashigin ruwan Suez da wasu a yankin Sinai dake makwabtaka da yankin cewa, rawar da sojoji ke takawa cikin irin wadancan ayyuka in ma akwai, to ita ce sa ido da kula da ayyukan.

Ayyukan sun hada da hanyoyin karkashin kasa a mashigin ruwan Suez da sabon birnin Ismailia da sabuwar cibiyar samar da ruwan sha ta birnin da sabon tafkin kamun kifi da hanyoyin da masu yawon bude ido za su bi a wajen tafkin da sabuwar kasuwar kifi da gadar da ta ratsa cikin ruwa da sauransu.

Shugaban ya kara da cewa, sojojin na kokarin tabbatar da an gudanar da ayyukan cikin lokacin da aka kayyade bisa tsarin raya kasa na kasar. yana mai cewa suna bukatar hukumar da za ta tabbatar da gudanar aikin a kan lokaci. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China