in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kotun Masar ta yanke hukuncin daurin shekaru 25 ga mutane 30 da ake zargi da ta'addanci
2019-03-31 16:43:52 cri
A ranar Asabar wata kotun kasar Masar ta yanke hukuncin daurin shekaru 25 a gidan yari ga wasu 'yan kasar su 30 bisa zarginsu da hannu wajen ayyukan da suka shafi ta'addanci da kuma alaka da kungiyar masu da'awar kafa daular musulunci ta (IS), kamfanin dillacin labaran kasar MENA shi ne ya bada rahoton.

Kotun dake shara'ar munanan laifuka ta Cairo ta zartar da hukuncin daurin shekaru 25 ga mutane 18 da kuma daurin shekaru 8 zuwa 15 ga wasu mutanen 4 sai kuma wasu mutanen 4 da aka yankewa hukuncin zaman gidan kaso na shekaru 10 bisa samunsu da laifin shiga kungiyar ta IS, tare da mallakar ababen fashewa da kuma yunkurin tarwatsa wani coki dake yankin tekun Alexandria.

Mai gabatar da shara'ar yana kuma zargin mutanen da yunkurin lalata wasu cibiyoyi tare da zargin da samun horon sojoji daga wajen mambobin kungiyar IS a kasashen Syria da Libya masu fama da yaki.

Ayyukan ta'addanci a Masar yayi sanadiyyar kashe daruruwan 'yan sanda, sojoji, da fararen hula tun bayan kifar da gwamnatin zababben shugaban kasar Mohamed Morsi a watan Yulin shekarar 2013 bayan da aka samu barkewar mummunar zanga zangar nuna kin jinin shugabancinsa na tsawon shekara guda da kuma haramta ayyukan kungiyarsa ta 'yan uwa musulmi wato Muslim Brotherhood.

Kungiyar IS wanda ke zaune a birnin Sinai, ta sha daukar alhakin kaddamar da mafi yawan hare haren ta'addanci da aka kaddamar a kasar Masar a 'yan shekarun da suka gabata.

Bugu da kari, jami'an tsaron kasar Masar sun hallaka daruruwan mayakan 'yan ta'addan, kana sun cafke dubban mutanen da ake zargi da hannu wajen ayyukan ta'addanci a kasar ta Masar tun bayan kifar da gwamnatin Morsi. (Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China