in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Masar da jami'in MDD sun tattauna batutuwan shiyya da yaki da ta'addanci
2019-04-04 10:12:36 cri

Shugaban kasar Masar Abdel-Fattah al-Sisi a ranar Laraba ya tattauna tare da babban sakataren MDD Antonio Guterres a yayin wata ziyara inda suka tattauna game da batutuwan da suka shafi shiyya da kokarin da ake wajen yaki da ayyukan ta'addanci.

Sisi da Guterres sun tattauna game da cigaban da aka samu na baya bayan nan a yankin gabas ta tsakiya, musamman a kasashen da aka fi fama da tashe tashen hankula wato kasashen Libya, Syria da Yemen, inji kakakin fadar shugaban kasar Masar Bassam Rady.

Taron ganawar ya samu halartar ministan harkokin wajen Masar Sameh Shoukry da shugaban hukumar tattara bayanan sirri na kasar Abbas Kamel.

Guterres ya shirya kai ziyara zuwa Libya bayan ziyararsa a birnin Alkahira na kasar Masar, gabanin babban taron da MDD ta shirya wanda zai lalibo hanyoyin da zasu taimaka wajen shirya zabe don kawo karshen tashin hankalin kasar ta Libya.

A wani taron manema labarai wanda Shoukry ya shirya bayana kammala ganawar, Guterres ya jaddada muhimmanci dake tattare da hada kan hukumomin kasar Libya, domin kaucewa dukkan wani fito na fito a kasar, da kuma samar da ingantaccen yanayin zaman lafiya a kasar ta Libya. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China