SIS ta fada cikin wata sanarwa cewa, ta kaddamar da shafin na Afrika ne da harshen Sinanci saboda a shekarun baya bayan nan ana samun karin mua'amalar hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika, sannan ana samun karin jarin da kamfanonin kasar Sin suke zubawa a kasashen Afrika masu yawa a dukkan fannoni.
Sanarwar ta ce shafin da aka kaddamar zai taimaka wajen samar da muhimman bayanai game da kungiyar tarayyar Afrika AU da hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afrika (FOCAC).
Shafin zai kuma samar da bayanai game da kasashen Afrika kuma zai dinga sabunta muhimman labaran Sin da Afrika, da sharhi da kasidu wadanda suka shafi hulda tsakanin bangarorin biyu, inji SIS.
Shafin na SIS a yanzu yana amfani da harsunan Sinanci, Larabci, Turanci, Faransanci, da yaren Sifaniya. (Ahmad Fagam)