in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jawabin Xi Jinping dangane da matasan kasar Sin ya karfafa gwiwar dalibai da suke karatu a ketare
2019-05-02 16:12:43 cri

Ranar 30 ga watan Afrilu, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya ba da muhimmin jawabi a yayin babban taron cika shekaru 100 da zanga-zangar neman dimokuradiyya da ilmin kimiyya da matasa suka yi. Jawabin Xi Jinping ya karfafa gwiwar matasan kasar Sin wadanda ke karatu da aiki a kasashen ketare, inda suka bayyana cewa, dole ne su sauke nauyin da aka dora musu a zamanin yau, su ba da nasu gudummawa wajen farfado da al'ummar Sinawa.

Wang Yuehan, wani dalibin da ke karatun digiri na uku a jami'ar Moscow ta kasar Rasha ya ce, muhimmin jawabin Xi Jinping ya karfafa gwiwar matasan kasar Sin da su yi kokarin cimma babban burin da suke fata, su kuma sauke nauyin da aka dora musu a zamanin yau. Tilas ne matasan kasar Sin su tuna da kalamin Xi Jinping a zukatansu sosai, su ba da nasu gudummawa a babban aikin raya kasar Sin ta zamani da karfafa tsarin gurguzu da kuma farfado da al'ummar Sinawa.

Sun Liyuan, wanda ke karatun digiri na biyu a jami'ar Long Island ta kasar Amurka ya nuna cewa, kasar Sin tana bai wa dalibanta da ke karatu a ketare goyon baya matuka, wadanda suke dogaro da ita sosai. Kishin kasa, shi ne ainihin ruhun tunanin zanga-zangar da aka yi a ranar 4 ga watan Mayun shekarar 1919, kana kuma ainihin ruhun al'ummar Sinawa. Kishin kasa ya karfafa gwiwar al'ummar Sinawa su hada kansu domin yin gwagwarmaya da tsayawa a kan kafafunsu. A matsayinsu na matasan kasar Sin na zamanin yau, dole ne su kara zage damtse a kokarin samar da sabbin abubuwan al'ajabi. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China