in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen Yamma sun yi kira da a ceto yarjejeniyar zaman lafiyar Sudan ta kudu
2019-05-01 15:35:47 cri
Kasashen Burtaniya da Norway da Amurka, sun yi kira ga bangarorin da yarjejeniyar zaman lafiyar kasar Sudan ta kudu da aka sanyawa a hannu a shekarar 2015 ta shafa, da su cimma matsaya su kuma ceto ta daga rugujewa.

Gamayyar kasashen uku da ake kira Troika, sun bayyana haka ne cikin wata sanarwar hadin gwiwa da suka fitar a jiya Talata, in suka bayyana cewa, yarjejeniyar tana fuskantar barazanar rushewa, muddin sassan da suka sanya hannu ba su kai ga warware bambance-bambance dake tssakaninsu game da kafa gwamnatin hadin kan kasa a wata mai zuwa ba.

Bugu da kari, kungiyar ta bukaci bangarorin da rikicin ya shafa da shugabannin shiyya, da su kara zage damtse wajen ganin sun ciyar da shirin wanzar da zaman lafiyar gaba.

Kungiyar ta kuma bayyana cewa, muddin sassan suna fatan cimma wannan buri a siyasance, akwai bukatar su yi aiki tare, ta hanyar gina aminci tsakanin shugabanni da al'ummomin kasar.

Kasashen uku sun ce, yarjejeniyar ta taimaka wajen rage tashin hankali a galibin sassan kasar, amma har yanzu fararen hula na dandana kunar fadan da ake ci gaba da gwabzawa, da kuma yadda ake ci gaba da gallazawa mata. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China