in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta nada sabon wakili a Sudan ta kudu
2016-12-14 09:56:45 cri
Babban sakataren MDD Ban Ki-moon ya sanar da nada David Shearer dan kasar New Zealand, a matsayin sabon wakilin musamman na MDD a Sudan ta kudu, kuma shugaban tawagar wanzar da zaman lafiya a Sudan ta kudu (UNMISS).

A wata sanarwa da ya fitar a Juba, babban birnin Sudan ta kudun, Ban yace Shearer zai maye gurbin Ellen Margrethe Loj 'yar kasar Denmark, wacce wa'adin aikinta ya kare a watan Nuwamban shekarar nan ta 2016.

Sanarwar ta ce Ban Ki-moon ya yabawa Loj saboda irin rawar data taka da kuma kyakkyawan shugabanci hukumar UNMISS sama da shekaru biyu da suka gabata, game da irin kalubalolin siyasa, tsaro, aikin jin kai, da kuma take hakkin bil adama da ya dabaibaye kasar ta Sudan ta kudu.

A halin yanzu Shearer wanda dan majalisar dokokin New Zealand ne, ya karbi sabon mukamin ne bayan ya yi murabus daga mukamin dan majalisar, inda zai fara aiki a ranar 31 ga watan Disamba.

Kafin ya a zabe shi dan majalisar dokokin New Zealand a shekarar 2009, Shearer, ya taba rike mukaman mataimakin wakilin musamman na sakatare janar na MDD, da ko'odinetan MDD, da kuma jami'in bada agaji na MDD a kasar Iraq tsakanin shekarun 2007 zuwa 2009.

A baya dai ya rike muklamai da dama a MDD.

Kuma ya yi rubuce rubuce da dama da suka shafi batun magance rikice rikice, da hanyoyin kai dauki don wanzar da zaman lafiya da kuma harkokin inganta rayuwar bil adama.

Sudan ta kudu ta fada cikin yakin basasa ne tun a watan Disamban shekarar 2013, bayan da dangantaka ta yi tsami tsakanin shugaban kasar Salva Kiir da korarren mataimakinsa Riek Macahr. Dubban mutane ne suka mutu, kana sama da mutane miliyan 2 rikicin ya raba da matsugunansu.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China