in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta nuna damuwa game da yawaitar cin zarafin jami'an bada agaji a Sudan ta kudu
2017-07-17 10:36:34 cri

Hukumar bada jin kai ta MDD ta koka saboda yawaitar kaddamar da hare hare kan jami'an bada agaji a Sudan ta kudu, inda ta bayyana cewa kimanin jami'an bada agajin 100 ne matsalar ta shafa kamar yadda ta bayyana cikin wani rahoto a watan Yuni, kuma wannan shi ne adadi mafi yawa da aka taba samu a cikin wata guda a shekarar nan ta 2017.

Ofishin kula da al'amuran jin kai na MDD (OCHA) ya bayyana cikin rahotonsa na baya bayan nan cewa, koda yake akwai raguwar tashe tashen hankula da matsalar tabarbarewar tsaro a wuraren da ake kai kayan agaji a watan Yuni, sai dai ba'a tura jami'an kai agajin ba a wannan watan, masu bada agajin na kasa da kasa sun koka game da yawaitar kaddamar da hari kan jami'anta da kayayyakin agajin, tun daga ranar 29 ga wata Mayu zuwa 26 ga watan Yuni.

Hukumar ta ce hare haren da ake kaddamarwa kan jami'an bada agajin da kayayyakin agajin ciki har da ballewa wajen adana kayan da kuma kwashe kayan agajin da aka samar da cin zarafin jami'an.

Bisa ga tanade tanaden dokokin kasa da kasa, kaddamar da hari kan jami'an raba kayan agaji babban laifi ne da ci karo da dokokin kasa da kasa. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China