in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya gana da takwaransa na Mozambique Filipe Nyusi
2019-04-24 14:13:39 cri

A yau Laraba ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da takwaransa na kasar Mozambique Filipe Nyusi a nan birnin Beijing.

A yayin ganawar shugaba Xi ya nuna cewa, yana maraba da halartar taron kolin tattaunawar hadin kai na kasa da kasa karo na biyu kan shawarar "Ziri daya da hanya" da shugaba Filipe Nyusi zai yi. A cewar shugaba Xi, kasar Mozambique muhimmiyar tsohuwar tashar hanyar siliki ce ta teku, kuma ta himmatu wajen shiga aikin raya shawarar "Ziri daya da hanya daya". Bangarorin biyu sun cimma matsaya kan inganta shirin shawarar tare, suna kuma kokarin hadin kai irin na samun moriya tare a tsakaninsu.

A nasa bangare Filipe Nyusi ya bayyana cewa, ya yi godiya sosai da taimakon da bangaren Sin ya baiwa kasarsa wajen agazawa wadanda mahaukaciyar guguwar nan ta Idai ta shafa. Ya kara da cewa, raya shawarar "Ziri daya da hanay daya" tare zai taimaka ga karuwar tattalin arzikin duniya da ci gaban duniya cikin daidaito, tana kuma da muhimmanci ga kasar Mozambique da ma nahiyar Afirka baki daya.

Bayan ganawar, shugabannin kasashen biyu sun kalli yadda jami'an bangarori biyu suka sanya hannu kan wasu takardun hadin kai a tsakanin, ciki har da shirin hadin kan raya shawarar "Ziri daya da hanya daya". (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China