in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Xi Jinping zai halarci taron koli na biyu BRI
2019-04-19 14:55:25 cri

Yau Jumma'a ranar 19 ga wata, wakilin majalisar gudanarwar kasar Sin, kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya kira taron manema labarai, inda ya sanar da cewa, za a yi taron koli na biyu na dandalin tattaunawar hadin kan kasa da kasa bisa shawarar "ziri daya da hanya daya" BRI daga ranar 25 zuwa ranar 27 ga wata a nan birnin Beijing. Inda shugaban kasar Sin Xi Jinping zai halarci bikin bude taron tare da ba da jawabi, sa'an nan zai shugabanci taron shugabanni na tattaunawa. Bayan taron kuwa, zai bayyana wa kafofin watsa labarai na gida da na waje sakamakon da za a samu a yayin taron.

Ban da wannan, Wang Yi ya furta cewa, taron na wannan karo na da ma'ana a fannoni biyar, wadanda suka hada da tsayawa ra'ayin kasancewar bangarori da dama, da habaka fannonin hadin kai, da raya tsarin abuta don samun ci gaba tare, da daukar matakai na a zo a gani, da ma more sakamakon da aka samu bayan aiwatar da manufar bude kofa ga waje da yin kwaskwarima a gida.

Bugu da kari, Wang Yi ya nuna cewa, ra'ayin samun dama bisa shawarar muhimmin jigo ne na hadin gwiwar kasa da kasa don samun nasara tare a halin yanzu. Babu hujja ko kadan ta shafa wa shawarar kashin kaji da cewa wai tana da manufar kafa tarkon basusuka, ta yadda ba za ta samu yarda wace kasar ta sa hannu ciki shawarar ba. Wang ya kara da cewa, ko wace kasa na da 'yancin sa hannu a cikin shawarar, amma ba wadda ke da hakkin hana saura su sa hannu a ciki. (Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China