in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An aiwatar da dukkan ayyukan da aka tsara a gun taron tattaunawa kan hadin gwiwar kasa da kasa masu bin shawarar "ziri daya da hanya daya" karo na farko
2019-04-22 20:05:01 cri
Ofishin rukunin shugabanni na aikin sa kaimi ga raya shawarar "ziri daya da hanya daya" ya gabatar da rahoto game da ci gaba da aka samu, da gudummawa da aka samar, da makoma da za a samu kan raya shawarar "ziri daya da hanya daya" a yau Litinin, inda aka bayyana cewa, an aiwatar da dukkan ayyuka 279 dake shafar fannoni 5 da aka tsara a gun taron tattaunawa kan hadin gwiwar kasa da kasa ta masu bin shawarar "ziri daya da hanya daya" karo na farko.

Rahoton ya shaida cewa, bisa tsarin hadin gwiwa wajen raya shawarar "ziri daya da hanya daya", Sin ta nuna goyon baya ga kasashen Asiya, da Afirka, da Latin Amurka da sauran kasashe masu tasowa wajen kara gina ayyukan more rayuwa, da samar da moriyar da aka samu a yayin da ake kokarin raya tattalin arzikin duniya gare su. Bisa sakamakon binciken da bankin duniya ya yi kan tsarin ciniki, yawan GDP na kasashen gabashin Asiya da yankin tekun Pasifik zai karu da kashi 2.6 zuwa 3.9 cikin dari ta hanyar raya shawarar "ziri daya da hanya daya". (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China