in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude cibiyar yada labarai ta babban dandalin tattaunawa kan shawarar ziri daya da hanya daya karo na biyu
2019-04-24 10:39:54 cri
A jiya ne, aka fara gwada cibiyar yada labarai ta babban taron dandalin tattaunawa na hadin-gwiwar kasa da kasa kan shawarar "ziri daya da hanya daya" karo na biyu a birnin Beijing.

An kafa cibiyar ce a babban dakin taron kasa da kasa na kasar Sin dake Beijing, wadda ta kunshi manyan dakunan taron manema labarai guda biyu, da wani wurin aiki mai fadin murabba'in mita 2200 tare da tebura 546 gami da kwafutoci 210.

Manema labarai za su kuma samu damar amfani da fasahar sadarwar zamani ta 5G a wajen.

Yanzu haka manema labarai sama da 4100, ciki har da 1600 daga kasashen ketare ne, suka yi rajistar aikin bayar da rahotanni game da taron, wanda za'a yi daga ranakun 25 zuwa 27 ga watan da muke ciki.

Cibiyar yada labaran za ta rika aiki ba tare ba rana tun daga karfe 6 na safiyar ranar 26 zuwa karfe 10 na daren ranar 27 ga wata. (Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China