in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
FATF: kasar Sin ta samu ci gaba wajen yaki da halatta kudin haram
2019-04-19 09:47:09 cri

Babban bankin kasar Sin ya bayyana a jiya cewa, kungiyar aiki ta musamman kan hada-hadar kudi ta FATF ta kaddamar da rahotonta a kwanan baya, inda ta ce, kasar Sin ta samu ci gaba wajen yaki da halatta kudin haram a shekarun baya. A cewarta kuma, kasar Sin ta dasa harsashi mai kyau ta fuskar tsarin yaki da halatta kudin haram.

Kungiyar FATF, kungiya ce mafi tasiri wajen yaki da halatta kudin haram da kuma tattara kudi domin aikace-aikacen ta'addanci, wadda kuma ta tsara ma'aunin yaki da halatta kudin haram a duniya.

Rahoton FATF ya ce, kasar Sin ta kafa tsarin kimanta barazanar halatta kudin haram a matakai daban daban, ta kuma tsara tare da aiwatar da manufar yaki da halatta kudin haram, tare da gudanar da tsarin tarurrukan yaki da halatta kudin haram tsakanin hukumomin gwamnati yadda ya kamata. Haka zalika kasar Sin ta samu ci gaba wajen sa ido kan halatta kudin haram a fannin aikin hada-hadar kudi, tare da samun sakamako wajen yaki da cin hanci, tattara kudi ba bisa doka ba, fataucin miyagun kwayoyi da sauran laifuffukan da suka shafi halatta kudin haram. Ban da haka kuma, kasar Sin ta na bada muhimmanci sosai, kan yaki da tattara kudi domin aikace-aikacen ta'addanci, ta na bin bahasin irin wadannan batutuwa da kai kara da gurfanar da masu laifi a gaban kotu. A fannin yin hadin gwiwa da kasashen duniya kuwa, kasar Sin ta kafa cikakken tsarin dokoki da kuma dawo da dimbin dukiyoyi daga ketare. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China