in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan kudaden da kasar Sin ta zuba wa kasashen da shawarar "Ziri daya da hanya daya" ta shafa ya zarce dala biliyan 90
2019-04-19 13:52:11 cri

Kakakin ma'aikatar kasuwancin kasar Sin Gao Feng ya bayyana jiya Alhamis, cewar daga shekarar 2013 zuwa ta 2018, yawan kudaden da kamfanonin kasar Sin suka zuba kai tsaye a kasashen da shawarar "ziri daya da hanya daya" ta shafa ya zarce dala biliyan 90, wanda matsakaicinsa ya karu da 5.2% a ko wace shekara. Sa'an nan jimillar darajar sabbin kwangilolin gini da kamfanonin kasar Sin suka kulla a kasashen ta zarce dala biliyan 600, wadda matsakacinta ya karu da kashi 11.9% a ko wace shekara.

Bisa kididdigar da ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin ta bayar a ranar, ya zuwa yanzu dai, kamfanonin kasar Sin sun kafa jerin yankunan hadin kan cinikayya a kasashen da shawarar ta shafa, yawan kudin da suka zuba a kansu kuwa ya zarce dala biliyan 30, lamarin da ya sa suka zama muhimmin dandali wajen sa kaimi ga karuwar tattalin arzikinsu da ma bunkasuwar masana'antunsu, har ma suka samar da guraben aikin yi kusan dubu 300.

Ban da wannan kuma, yin ciniki a Intanet ya zama wata sabuwar hanya wajen hadin kan kasa da kasa, kawo yanzu dai, kasar Sin ta riga ta kafa tsarin hadin kan yin ciniki ta Intanet da kasashe 17. (Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China