in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Manzon kasar Sin ya yi kira da a hada kai wajen yakar masu samarwa 'yan ta'adda kudade
2019-03-29 10:00:03 cri
Wakilin din-din-din na kasar Sin a MDD, Ma Zhaoxu, ya yi kira ga al'ummomin kasashen duniya, da su kara yin hadin gwiwa da samar da kwarewa tsakanin kasashen mambobin majalisar a yayin da ake yakar masu daukar nauyin ayyukan ta'addanci.

Ma wanda ya yi wannan kira yayin bude zaman muhawarar kwamitin sulhun MDD, ya ce yakar masu daukar nauyin ayyukan ta'addanci, batu ne mai sarkakiyar gaske, kuma galibin kasashe masu tasowa ba su da kudade ko kwarewar yakar wannan matsala.

Ya ce, muddin ba a fatan ganin kowa ce kasa ta shiga wannan tarko, sakamakon barazana daga ketare ko waje, da tsohe duk wata kafa da 'yan ta'adda za su samu kudade, ya kamata al'ummomin kasashen duniya su kara taimakawa kasashe mambobin MDD da kudade da dabaru.

Ma ya ce, kasar Sin za ta kara bullo da matakai na toshe duk wasu hanyoyi da 'yan ta'adda ke samun kudade, ta hanyar bayanan sirri, da sanya-ido da musayar bayanai.

Ya ce, kasar Sin tana dora muhimmanci matuka kan kandagarki da ma hana 'yan ta'adda samun kudade, ta hanyar karfafa matakan sanya ido wajen hana satar kudade, daukar nauyin ayyukan ta'addanci, da kaucewa biyan haraji.

Ya kara da cewa, kasar Sin, za ta hada kai da kungiyoyin kasa da kasa,da samarwa kasashe maso tasowa taimakon kwarewa, gwargwadon karfinta, za kuma ta yi aiki da sauran kasashe wajen ganin an ga bayan masu daukar nauyin ayyukan ta'addanci, da yaki da ayyukan ta'addanci, ta yadda za a samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China