in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rahoto: Dokar zuba jari ta baki za ta janyo masu zuba jari a kasar Sin
2019-03-28 11:08:39 cri
Wani sabon rahoto da kamfanin kula da dokoki na kasa da kasa mai suna Linklaters ya fitar, ya nuna cewa, ana sa ran jarin waje ta hanyar hadin gwiwa da sayen kamfanoni (M&A) a kasar Sin zai kai dala triliyan 1.5 nan da shekaru 10 masu zuwa.

Rahotan ya kuma yi hasashen cewa, jarin da ake sa ran zubawa a kasar, zai ninka na shekaru goman da suka gabata fiye da sau uku, yayin da sabbin dokoki, ciki har da sabunta wasu fannonin zuba da aka yi da dokar zuba jari ta baki 'yan kasuwa da su saukaka zuba jari a wasu muhimman bangarori kamar hada-hadar kudade da masana'antun kera ababan hawa.

Manufar dokar zuba jari ta baki 'yan kasuwa da majalisar wakilan kasar ta amince da ita, ita ce samar da kyakkyawan yanayi na kasuwanci ga baki masu sha'awar zuba jari a cikin kasar.

Shugaban kamfanin na Linklaters Charles Jacobs, ya bayyana cewa dokar zuba jari ta baki 'yan kasuwa, doka ce dake da Muradin kare 'yancin baki masu zuba jari da tambarin hajojinsu, za kuma ta ba su damar zuba jari a kasar Sin, ta hanyar yin hadin gwiwa, da taimakawa kamfanonin kasar Sin fadada rassansu.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China