Mataimakin firaministan kasar Croatia kana ministan kula da ayyukan gona na kasar, Tomislav TOLUŠIĆ ya ce, a matsayin kasar da ta karbi bakuncin shawarwarin a wannan karo, Croatia ta samu kyakkyawan zarafin nuna kanta ga nahiyar Turai har ma ga duk duniya baki daya.
Ya ce Croatia da Sin suna da moriya ta bai daya da dama, kuma ya kamata su aiwatar da hadin-gwiwa a wasu fannoni da dama, wadanda za'a tabbatar da su bayan shawarwarin.
Shi ma a nasa bangaren, mataimakin shugaban hukumar bunkasa fasahohin sadarwa ta gwamnatin kasar Hungary Andre Schipaler yana ganin cewa, kasar Sin na samar da babban karfi ga ci gaban tattalin arzikin duniya, yana mai cewa, idan wata kasa na son samun ci gaba, hadin-gwiwa da kasar Sin na da muhimmancin gaske. Shi kuma ya yabawa irin muhimmancin da kasar Sin ke bawa yankunan tsakiya gami da gabashin nahiyar Turai, har ma yana da yakinin cewa hadin-gwiwar Hungary da Sin na da karin damammaki.(Murtala Zhang)