in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta yi shawarwari tare da bangarori daban-daban don yin hadin-gwiwa a fannin shawarar "ziri daya da hanya daya"
2019-04-15 20:37:46 cri
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang ya bayyana yau Litinin a Beijing cewa, kasarsa za ta yi shawarwari tare da bangarori daban-daban ciki har da kasashen nahiyar Turai, don daukar matakan hadin-gwiwa wajen aiwatar da shawarar "ziri daya da hanya daya".

Lu Kang ya ce, kawo yanzu, kasashe 16 dake yankin tsakiya gami da gabashin nahiyar Turai, tare kuma da kasar Girka, sun rattaba hannu tare da kasar Sin kan takardar hadin-gwiwa a fannin "ziri daya da hanya daya", kana, Italiya da Luxembourg da wasu sauran kasashen Turai su ma sun daddale takardar bayani kan hadin-gwiwar shawarar "ziri daya da hanya daya" tare da kasar Sin.

Lu ya kara da cewa, za'a kaddamar da babban dandalin tattaunawa kan hadin-gwiwar kasa da kasa ta fuskar shawarar "ziri daya da hanya daya" karo na biyu a karshen mako mai zuwa a Beijing, inda shugabannin kasashe daban-daban gami da wasu manyan wakilan nahiyar Turai za su hallara. Kasar Sin za ta gudanar da shawarwari kan matakan hadin-gwiwa da za ta dauka tare da bangarori daban-daban, ciki har da kasashen Turai, don bunkasa shawarar "ziri daya da hanya daya", ta yadda hadin-gwiwarsu za ta ci gaba da habaka ba tare da wata matsala ba.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China