in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kammala bikin baje kolin kasa da kasa kan aikin gona a Morocco
2019-04-22 11:01:12 cri
Jiya ne a birnin Meknes dake arewacin kasar Morocco, aka kammala bikin baje kolin kasa da kasa kan aikin gona da aka saba gudanarwa kowace shekara a kasar, bikin da ya hallara baki da mahalarta bikin masu tarin yawa.

Da yake yiwa taron manema labarai karin haske, kwamishina mai kula da bikin baje kolin, Jaouad Chami, ya bayyana cewa, kimanin mutane 850,000 ne suka halarci bikin da aka bude a ranar Talatan da ta gabata, inda mutane 32,000 suka halarci bikin a ranar Asabar din da ta gabata.

Bikin baje kolin mai taken, "aikin gona, aikin yi da makomar yankunan karkarar duniya" ya samu halartar masu baje koli 1,500 daga kasashe 60, inda kasar Switzerland ta halarci bikin a matsayin bakuwa ta musammam a wannan karo.

Tun lokacin da aka fara bikin a shekarar 2006, bikin baje kolin kasa da kasa kan aikin gona, ya kasance mai muhimmanci ga bangaren aikin gonar kasar Morocco da ma Afirka.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China