in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Morocco ta dakile yunkurin bakin haure
2019-01-03 09:26:39 cri
'Yan sanda a kasar Morocco sun sanar a jiya Laraba cewa sun yi nasarar dakile wani yunkurin da wasu bakin haure suka shirya wanda ya kunshi mutane kimanin 89.

A lokacin da 'yan sanda suka kai samame a birnin Sale, a kusa da babban birnin kasar Rabat, an damke mutane uku da ake zargi da hannu wajen shirya badakalar bakin hauren, in ji wata sanarwa daga jima'an yan sandan.

Bakin hauren, wadanda dukkanninsu sun fito ne daga birnin El Youssoufia, sun biya kudade tsakanin dala 500 zuwa 1,500 da nufin a tsallaka da su Turai ta barauniyar hanya.

Morocco ta fuskanci karuwar bakin haure ta barauniyar hanya cikin shekarar da ta gabata.

A cewar ma'aikatar harkokin cikin gidan Morocco, hukumomin kasar sun yi nasarar dakile yunkurin bakin haure kimanin 76,000 tsakanin watan Janairu zuwa Nuwamban shekarar data gabata.

A cikin wannan lokacin, kasar ta kuma dakile wasu hadakar tawagogin bakin hauren kimanin 174, wanda ya karu daga adadin tawagogi 70 a shekarar 2017. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China