A bana ake cika shekaru 70 da kafa sabuwar kasar Sin, don hakan taken bikin nuna fina-finan kasa da kasa na Beijing a wannan karo shi ne "gida da kasa". Bisa ka'idojin "more fasahohi da yin kokarin samun kyakkyawar makoma tare", an sa kaimi ga yin mu'amala da hadin gwiwa da juna a tsakanin masu tsara fina-fina na Sin da na kasashen waje. A yayin bikin, jimilar fina-finai 775 daga kasashe da yankuna 85 ne suka shiga takarar neman samun lambar karramawa mai suna Tiantan. Bayan zabe sau da dama, fina-finai 15 daga kasashe da yankuna 20 ne suka shiga takara ta zagayen karshe don neman samun lambar karramawa ta Tiantan. (Zainab)