in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi bikin fina-finai a Shanghai mai jigon "Ziri daya da hanya daya"
2018-06-21 11:06:08 cri
A daren jiya 20 ga wata, wajen bikin fina-finan birnin Shanghai na kasa da kasa an gabatar da wani biki na musamman na daren fina-finai mai jigon "Ziri daya da hanya daya", inda aka samar da manyan lambobin yabo wato fina-finai mafiya karbuwa, fina-finai mafi jawo hankalin kafofin yada labarai da masu aikin fina-finai mafiya karbuwa. Ban da wannan kuma, an kafa kungiyar bikin fina-finan "Ziri daya da hanya daga" a wannan rana da dare.

Bikin fina-finan da aka yi a wannan karo, wanda ake dinga gudanar da shi cikin shekaru da dama, ya yi sauyawar fasali sosai bisa tushen mu'ammalar al'adun da aka saba yi a baya, inda aka kafa makon fina-finan "Ziri daya da hanya daya", matakin da ya kasance wani sabon abu mai muhimmanci sa aka samu a bikin wannan karo.

An bada labarin cewa, kasashen da shawarar "Ziri daya da hanya daya" ta shafa za su kara tuntubar juna da kara mu'ammala tsakaninsu ta fuskar al'adu da fasahohi bisa tushen fina-finai, karkashin kungiyar da aka kafa a wannan rana, da kuma sa kaimi ga baje kolin fina-finai a bukukuwan fina-finan kasashe daban-daban da dai sauransu. (Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China