Wasu finai-finai gami da shirye-shiryen talabijin na kasar Sin wadanda suka shafi zaman rayuwar Sinawa ko kuma ci gaban da kasar Sin ta samu, da aka fassara su zuwa harsunan Turanci da Rashaci da Larabci sun jawo hankalin jama'a.
Kawo yanzu, kasar Sin ta fassara fina-finanta da yawansu ya zarce dari uku, da shirye-shiryen talabijin sama da dubu bakwai daga yaren Sin zuwa wasu harsuna 23, wadanda aka nuna su a nahiyoyin Asiya da Afirka da Turai da Amurka da sauransu.(Murtala Zhang)