Babban gidan rediyo da talabijin na kasar Sin ya samar da fasahar sadarwa ta 5G a yayin bikin, kuma irin fasahohin sadarwar zamanin da yake amfani da su sun kara kyautata ayyukan yada labarai game da bikin.
A yayin bikin, jimilar fina-finai 775 daga kasashe da yankuna 85 ne suka shiga takarar neman samun lambar karramawa mai suna Tiantan. Kana kuma za'a nuna wasu fina-finan gida da waje kusan dari biyar a sinima 30 dake Beijing. Har wa yau, a yayin bikin, za'a kaddamar da dandalin tattaunawa kan fina-finan da suka shafi murnar cika shekaru 70 da kafa Jamhuriyar Jama'ar kasar Sin, da makon fina-finan Indiya, da sauran makamantansu. Za'a kuma bayar da babbar lambar karramawa ta Tiantan yayin da ake rufe bikin, wanda zai shafe tsawon mako daya.(Murtala Zhang)