in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Taron koli na biyu na dandalin tattaunawar hadin kan kasa da kasa bisa shawarar BRI zai ciyar da shawarar gaba
2019-04-19 21:10:35 cri

Yau Jumma'a ne, wakilin majalisar gudanarwar kasar Sin, kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya kira taron manema labarai, inda ya sanar da cewa, za a yi taron koli na biyu na dandalin tattaunawar hadin kan kasa da kasa bisa shawarar "ziri daya da hanya daya" BRI daga ranar 25 zuwa ranar 27 ga wata a nan birnin Beijing. inda shugaban kasar Sin Xi Jinping zai halarci bikin bude taron tare da ba da jawabi, shugabanni kasashe ko gwamnatoci 37 ne, ake saran za su halarci taron. Wang ya bayyana cewa, yayin taron za a mayar da hankali kan batun inganta shawarar "Ziri daya da hanya daya" don samun ci gaba mai inganci.

Taron dandalin tattaunawar hadin kan kasa da kasa bisa shawarar "Ziri daya da hanya daya", na daga cikin dandalin hadin kan kasa da kasa mafi muhimmanci, taron dandalin na wannan karo zai kasance wani gagarumin taron na kasa da kasa. Ya zuwa yanzu, baki kusan dubu biyar da suka fito daga kasashe sama da 150 da kungiyoyin kasa da kasa sama da 90 ne suka tabbatar da halartar taron, yawansu ya wuce na taron farko. A yayin taron manema labarun da aka shirya a yau, Wang Yi ya bayyana cewa,

"Shugaba Xi Jinping zai halarci bikin bude taron tare da yin jawabi, sa'an nan zai shugabanci taron tattaunawar shugabanni. Bayan taron kuma, zai bayyana wa kafofin watsa labarai na gida da na waje sakamakon da ake fatan samu a yayin taron."

Wang Yi ya kara da cewa, babban taken taron shi ne, "raya shawarar 'Ziri daya da hanya daya', da kuma kafa makoma mai kyau". Bangarori daban daban za su tattauna kan wasu muhimman batutuwa, ciki har da kara yin cudanya da mu'amala, da nemo sabbin matakan ci gaba, da karfafa hadin kan manufofi, da kara kulla dangantakar abokantaka, da kara bullo da matakan samun dauwamamman ci gaba na tsimin makamashi da kuma tabbatar da ajandar MDD nan da shekarar 2030. Wang Yi ya jaddada cewa,

"A yayin da ake tattauna wadannan muhimman batutuwa, za a dora muhimmanci kan tabbatar da samun ci gaba mai inganci game da shawarar 'Ziri daya da hanya daya'. Wannan wata muhimmiyar manufa ce da shugaba Xi Jinping ya gabatar ga duk duniya, zai kuma nuna fatan irin daya na kasashen dake cikin ayyukan raya shawarar 'Ziri daya da hanya daya', ya kuma kafa burin da suke kokarin cimmawa, bisa jagorancinsa ne za a shiga wani sabon mataki na raya shawarar tare."

Bayan shekaru 6 da soma gabatar da shawarar "Ziri daya da hanya daya", yanzu, shawarar ta kasance wani dandalin hadin kan kasa da kasa dake shafar bangarori da dama. Alkaluman kididdiga na nuna cewa, yanzu jimilar kudin cinikayya a tsakanin kasar Sin da kasashen dake raya shawarar tare da kasar Sin, ta zarce dalar Amurka triliyan shida", yawan jarin da aka zuba ya wuce dalar Amurka biliyan 80.

Game da nasarorin da za a cimma a yayin taron dandalin tattaunawar, Wang Yi ya bayyana cewa,

"Za a bayar da wata hadaddiyar sanarwa a taron kolin tattaunawar, don nuna ra'ayin bai daya na shugabannin kasashe daban daban game da raya shawarar 'Ziri daya da hanya daya' tare, hakan za ta kasance nasara mafi muhimmanci ta dandalin tattaunawa a wannan karo. Baya ga haka, za a shirya babban taron masana'antu, inda za a gayyaci wakilan kamfanoni da na majalisun cinikayya na wasu kasashen da batun ya shafa, wadanda yawansu zai kai kimanin 800. A lokacin babban taron, jama'a daga fannin masana'antu da kasuwanci na kasashe daban daban za su cimma jerin yarjejeniyoyi na hadin gwiwa." (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China