in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wata dalibar Najeriya ta yaba da shawarar "ziri daya da hanya daya" ta kasar Sin
2019-01-28 15:20:18 cri


A halin yanzu ana gudanar da hadin-gwiwa da mu'amala sosai tsakanin kasar Sin da tarayyar Najeriya a fannoni daban-daban, kana kuma akwai 'yan Najeriya daga hukumomi da bangarori daban-daban wadanda ke zuwa samun horo a kasar Sin, Eugenia Chinenye Ndukwe mai shekaru 35 da haihuwa na daya daga cikinsu. A halin yanzu, tana kokarin neman samun digiri na uku a fannin alakar kasa da kasa a jami'ar Jilin ta kasar Sin, inda ta yaba sosai da shawarar "ziri daya da hanya daya" gami da ra'ayin raya kyakkyawar makomar bil'adama ta bai daya.

Bisa yarjejeniyar da aka daddale tsakanin Sin da Najeriya a karkashin tsarin dandalin tattaunawa kan hadin-gwiwar Sin da Afirka wato FOCAC a takaice, kasashen biyu na kara yin mu'amala da hadin-gwiwa ta fannin horar da jami'ai. Sashin kula da harkokin tattalin arziki da kasuwanci na ofishin jakadancin Sin dake Najeriya ya kan zabo wasu 'yan Najeriya a kowace shekara don su yi karatu ko samun horo a kasar Sin a fannonin da suka shafi ababen more rayuwar jama'a, da harkokin jiragen kasa, da ayyukan sadarwar zamani da ilimin diflomasiyya da sauransu. Zuwa shekara ta 2018, akwai 'yan Najeriya sama da 4300 wadanda suka samu damar karbar horo a kasar Sin.

A farkon shekara ta 2016, Eugenia Chinenye Ndukwe, jami'a ce daga cibiyar nazarin harkokin wutar lantarki ta ma'aikatar wutar lantarki da ayyuka da gidaje ta tarayyar Najeriya, ta samu damar halartar wani kwas din karawa juna sani a fannin diflomasiyya a kasar Sin, al'amarin da a cewarta, ya sauya zaman rayuwarta sosai, har ma ta kara fahimtar tsarin gwamnatin kasar Sin. Eugenia ta bayyana cewa:

"Ina mamakin yadda kasar Sin ta iya samun saurin ci gaba da dimbin nasarori kamar haka, kuma halartar kwas din horo a wancan karo ya karfafa mini gwiwa don kara sanin harkokin diflomasiyyar kasar Sin, inda na fahimci ainihin dalilin da ya sa harkokin diflomasiyyar Sin suka jawo hankalin mutane sosai, wato diflomasiyya ce da ake yi bisa tushen shawarwari da mu'amalar juna."

Har wa yau kuma, Eugenia Chinenye Ndukwe ta samu kyautar kudin karatun digiri na biyu da na uku a jami'ar Jilin ta kasar Sin, al'amarin da ya ba ta kyakkyawar damar kara nazarin harkokin kasar Sin, musamman a fannin diflomasiyya. Eugenia Chinenye Ndukwe ta ce:

"Ina so in yi magana kan shawarar 'ziri daya da hanya daya', wato muhimmiyar shawara ce da gwamnatin kasar Sin ta fitar don bunkasa tattalin arziki da inganta muhimman ababen more rayuwar jama'a a kasashen da abun ya shafa, kana wani muhimmin fanni ne a cikin harkokin diflomasiyyar kasar Sin. A ganina, ya kamata kowa da kowa ya jinjina wannan. Kasar Sin na nunawa duk fadin duniya irin zaman jituwa da adalci da ra'ayin jin kai da hakurin da take da su, wadanda suka zama tamkar ginshikai wajen raya huldar diflomasiyya tsakanin Sin da kasashe daban-daban."

A yayin da take karatu a kasar Sin, Eugenia ta taba ziyartar wasu birane da garuruwa da dama, don kara fahimtar al'adun kasar. A lokacin da take neman samun digirinta na biyu a jami'ar Jilin, ta kafa kungiyar tallafawa marasa karfi ta daliban kasashen waje dake karatu a jami'ar mai suna iCare, don taimakawa tsoffi da yara da koyar da harshen Turanci ba tare da karbar kudi ba. Ta kuma wakilci jami'arta don halartar wasu taruka a Majalisar Dinkin Duniya. Game da ra'ayin raya kyakkyawar makomar bil'adama ta bai daya da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar, Eugenia ta ce ra'ayin ya burge ta kwarai da gaske:

"A halin yanzu, kasar Sin na bada shawarar 'raya kyakkyawar makomar bil'adama ta bai daya', don neman samun bunkasuwa da moriyar juna, abun da zai taka muhimmiyar rawa a duk duniya. Kasar Sin na kara taka rawar gani a duniya, kuma tana gudanar da harkokin diflomasiyyarta yadda ya kamata ta hanyoyi daban-daban, ciki har da samar da horo da kwasa-kwasai gami da kyautar kudin karatu. Dukkan wadannan abubuwa sun shaida cewa, muna da kyakkyawar makomar bil'adama ta bai daya, kuma ina fatan za mu himmatu tare don cimma wannan babban buri."(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China