in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shawarar "ziri daya da hanya daya" na taimakawa ga hadin-gwiwar Sin da Afirka
2018-07-24 20:36:32 cri
Da daren ranar 23 ga wata, agogon wurin, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya isa birnin Pretoria, inda ya fara ziyarar aiki a kasar Afirka ta Kudu. A baya, shugaba Xi ya kammala rangadin aiki kasashen Senegal da Rwanda, kana kuma zai ratsa ta Mauritius a hanyarsa ta dawowa gida, don ziyartar kasar.

Daga kasar Senegal dake yammacin nahiyar Afirka, zuwa kasar Rwanda dake tsakiyar nahiyar, daga baya sai Afirka ta Kudu dake kudancin nahiyar, da kuma Mauritius, tsibiri dake gabashin Afirka, kowace kasa na da nata salo na musamman, wadanda dukkansu ke kokarin shiga shawarar "ziri daya da hanya daya", kuma sun samu nasara.

Kasar Sin da kasashen Afirka daban-daban na da mabambantan halin da ake ciki, kuma ci gaban tattalin arziki gami da zaman rayuwar al'umma ba daya ba ne, amma suna da ra'ayi iri daya wajen neman bunkasuwa da samun wadata da karfi.

Yau da shekaru biyar da suka shige, shugaba Xi Jinping ya ziyarci Afirka a karo na farko, inda ya bayyana manufofin gwamnatinsa kan Afirka, wato "nuna gaskiya, sakamako na hakika, da abuta, da sahihanci". Ma'anar manufofin sun hada da, nuna gaskiya ga abokan kasashen Afirka, da neman samun sakamako na hakika yayin da ake yin hadin-gwiwa tsakanin Sin da Afirka, da karfafa abokantaka tsakanin Sin da Afirka, tare kuma da nunawa kasashen Afirka sahihanci wajen yin hadin-gwiwa tare da su. A cikin shekaru biyar da suka gabata, sakamakon wadannan manufofi, hadin-gwiwa da zumunci dake tsakanin Sin da Afirka na dada samun ingantuwa. Akwai kasashen Afirka da dama wadanda suka bayyana niyyarsu ta shiga cikin shawarar "ziri daya da hanya daya".

Ba sau daya ba kuma ba sau biyu ba shugaban kasar Senegal Macky Sall, da takwaransa na kasar Rwanda Paul Kagame sun bayyana cewa, suna goyon-bayan shawarar "ziri daya da hanya daya", da nuna himma da kwazo wajen karfafa mu'amala da cudanya a tsakaninsu da kasar Sin.

Akwai muhimman dalilan da suka sa kasashen Afirka ke matukar son shiga shawarar "ziri daya da hanya daya". Na farko, kasashen Turai da Amurka na janye kamfanoninsu dake nahiyar Afirka, abun da ya sa kasashen Afirka da dama ke juya hankalinsu zuwa kasar Sin. Musamman bayan da Donald Trump ya zama shugaban Amurka, kasarsa ba ta maida hankali sosai kan nahiyar ta Afirka ba, haka kuma kasashen Turai na fuskantar matsalolin 'yan gudun-hijira da hare-haren ta'addanci, abun da ya sa suka kara maida hankali kan harkokin cikin gida, maimakon harkokin kasashen waje. Dalili na biyu shi ne, yayin da suke kokarin sauya salon raya tattalin arziki, kasashen Afirka na kara fuskantar matsin lamba har ma suna fatan yin hadin-gwiwa da kasar Sin. Akwai kasashen Afirka da dama wadanda suke fatan kasar Sin za ta gaggauta fitar da fasahohin zamani zuwa kasashen Afirka bisa shawarar "ziri daya da hanya daya", da samar da karin guraban ayyukan yi, da taimakawa ga canzawar salon raya tattalin arziki na nahiyar ta Afirka. Na uku, ana amfani da shawarar "Ziri daya da hanya daya" don canja halin da Afirka ke ciki na raguwar samun aikin yi a fannin masana'antun kere-kere.

Daga shekaru 80 na karnin da ya wuce har zuwa yanzu, a karkashin jagorancin kasashen yamma na "yin kwaskwarima kan tsare-tsare", kasashen Afirka sun kyautata tsarin ci gaban tattalin arziki sau da yawa, amma ba su samu nasara ba, hakan ma ya sa har yanzu nahiyar ke matsayin gefe kan tattalin arzikin duniya, har ma an bullo da alamar raguwar samun guraban aikin yi a fannin masana'antun kere-kere. Kason kudin da aka samu daga wajen samar da kaya na masana'antun kere-kere bisa na GDP ya karu daga 18% a shekarar 1975, zuwa kashi 11% a shekarar 2015.

Shawarar "Ziri daya da hanya daya" da Xi Jinping ya gabatar na hade da hadin kan masana'antu, da kaurar da masana'antu da dai sauransu, wadda kasashen Afirka ke mai da ita wata babbar dama mai kyau wajen tabbatar da raya masana'antu a babbar nahiyar Afirka.

An aza harsashi mai kyau na hadin kai ga kasashen Afirka wajen shiga ayyukan shawarar "Ziri daya da hanya daya". Da farko, kasar Sin da kasashen Afirka na kokarin neman kafa al'umma mai kyakkyawar makoma, suna da ra'ayin bai daya na neman ci gaba, kuma suna hadin kai sosai kan shirye-shiryen neman ci gaba. Bisa tsarin hadin kai da ake aiwatarwa tsakanin Sin da Afirka, wanda ke hade da kafa "manyan tsare-tsaren sufuri guda uku", ciki har da jiragen kasa masu saurin gaske, manyan hanyoyin mota da kuma zirga-zirgar jiragen sama a yankin, da raya masana'antu a fannin manyan kayayyakin more rayuwar jama'a, da kuma "Shirin hadin kai a fannoni guda 10 tsakanin Sin da Afirka", dukkan su ana iya ganin abubuwan hadin kai a fannin manyan kayayyakin more rayuwa a cikinsu. A sa'i guda kuma, Afirka na sa himma wajen hadin kai da kasar Sin; Ga misali, a cikin ajandar kungiyar AU nan da shekarar 2063, an gabatar da buri na tabbatar da raya masana'antu, inda aka mai da kasar Sin a matsayin muhimmin karfi da nahiyar za ta dogara da ita.

Yanzu nahiyar Afirka ta kasance wani muhimmin sashe na shawarar "Ziri daya da hanya daya", bayan 'yan shekarun da suka gabata, ta riga ta kasance nahiyar dake cimma karin nasarori wajen shawarar "Ziri daya da hanya daya". Ga misali, layin dogo daga garin Addis Ababa zuwa garin Djibouti dake hade da kasashen Habasha da Djibouti, da layin dogo daga birnin Mombasa da birnin Nairobi dake hade da Nairobi, babban birnin kasar Kenya da tashar ruwa Mombasa ta kasar, da dai sauransu, wadanda kasar Sin ce ta dauki nauyin gina su, dukkansu sun riga sun soma aiki.

A ranar 21 ga watan Yuli, a idannun shugaba Xi Jinping da shugaba Macky Sall, kasashen Sin da Senegal suka sa hannu kan takardar hadin kai ta raya ayyukan shawarar "Ziri daya da hanya daya", ta yadda kasar Senegal ta kasance kasa ta farko a yammacin Afirka, da ta sa hannu kan wannan takadar hadin kai da Sin. A ranar 23 ga wata kuma, a kan idanun shugaba Xi Jinping da takwaransa na kasar Rwanda Paul Kagame, aka sa hannu kan jerin takardun hadin kai a bangarori biyu, dake shafar batun raya "Ziri daya da hanya daya" da dai sauransu.

Mutane na da damar yin dako, bisa nasarorin da aka ta samu a fannin ayyukan raya shawarar "Ziri daya da hanya daya" a nahiyar Afirka. Hakan zai tabbatar da samun sabon ci gaba kan shawarar a duk nahiyar ta Afirka, za kuma a karfafa al'umma mai kyakkyawar makoma ga Sin da Afirka. (Murtala Zhang, Bilkisu Xi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China