in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bikin fina-finan kasa da kasa na Beijing ya taimaka wajen cudanyar al'adu bisa shawarar ziri daya da hanya daya
2019-04-17 10:51:06 cri

A halin da ake ciki yanzu, shawarar ziri daya da hanya daya tana kara samun karbuwa daga kasashen duniya, haka kuma cudanyar al'adun dake tsakanin kasa da kasa ita ma tana kara zurfafuwa sannu a hankali, fina-finai su ma suna taka rawar gani a wannan bangaren, a don haka ana iya cewa, bikin nunin fina-finan kasa da kasa na birnin Beijing karo na 9 da ake gudanarwa yanzu haka, yana taimakawa matuka wajen cudanyar al'adun tsakanin kasashen da suka shiga shawarar ziri daya da hanya daya.

Domin biya bukatun aiwatar da shawarar ziri daya da hanya daya, an shirya wani sashe na musamman mai taken "ziri daya da hanya daya" yayin bikin nunin fina-finan kasa da kasa na Beijing karo na 9, inda ake kokarin kara karfafa cudanyar al'adu tsakanin kasashen da suka shiga shawarar, tare kuma da kara zurfafa zumuncin dake tsakanin al'ummomin kasashen baki daya.

Bisa zurfafuwar aikin aiwatar da shawarar ziri daya da hanya daya, nan gaba za a kaddamar da karin hadin gwiwa wajen samar da fina-finai dake tsakanin kasar Sin da sauran kasashen duniya, hadin gwiwar da za ta ingiza ci gaban sha'anin samar da fina-finai na kasashe daban daban, ta hanyar yin musanyar albarkatun fina-finai tsakanin kasashe biyu ko kasashe fiye da biyu, ta haka ne kuma za a daga matsayin samar da fina-finai daga duk fannoni, har a kai ga cimma burin samar da karin fina-finai masu inganci, wadanda za su kara samun karbuwa daga wajen masu kallo a fadin duniya.

Hakika babbar manufar aiwatar da shawarar ziri daya da hanya daya ita ce, ingiza hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa, ta yadda za a samu wadata tare, haka kuma babbar manufar shirya bikin nunin fina-finan kasa da kasa na Beijing ita ce, cimma burin samun wadatar kasuwar al'adun fina-finan kasar Sin, gami da kasuwar al'adun fina-finan kasa da kasa baki daya.

A cikin 'yan shekarun da suka gabata, masu aikin samar da fina-finai na kasar Sin, suna kokarin neman samun damar hadin gwiwa tsakaninsu da na kasashen ketare. A sa'i daya kuma, suna kokarin shiga aikin samar da fina-finai a ketare ta hanyar zuba jari a fannin. Misali kamfanin samar da fina-finai na Alibaba na kasar Sin, ya zuba jari a cikin aikin samar da fim din "Green Book", wanda ya samu lambobin yabo guda uku na kwarewa na Amurka wato Oscars. Hakan ya sa kamfanonin kasar Sin suka samu babban sakamako a kasuwar fina-finan kasa da kasa, har ya sa al'adun kasar Sin suka kara samun karbuwa daga wajen al'ummomin kasashen duniya.

Yanzu ba ma kawai kamfanonin kasar Sin suna gudanar da hadin gwiwa a bangarorin zuba jari da kuma samar da fina-finai tsakaninsu da kamfanonin kasashen ketare ba ne, har ma suna sayar da fina-finai da wasan kwaikwayo na kasar zuwa ga kasuwar ketare lami lafiya. Amma kafin a fara aiwatar da shawarar ziri daya da hanya daya, akwai wahala matuka a sayar da fina-finan kasar Sin zuwa kasuwar ketare, sakamakon kayyade cinikayya, da kuma bambancin al'adun dake tsakanin kasa da kasa. Yanzu haka yanayin ya sauya, bisa habakar shawarar ziri daya da hanya daya, cudanyar dake tsakanin kasar Sin da sauran kasashen duniya a fannin samar da fina-finai tana kara zurfafuwa, baya ga aminci da fahimtar juna a bangaren al'adu dake tsakanin sassan biyu wadanda su ma suke kara karfafuwa sannu a hankali. Misali fina-finan kasar Sin sun fi samun karbuwa daga wajen 'yan kallo na nahiyoyin Afirka da Oceania da Latin Amurka da sauransu.

Abu mai faranta rai shi ne shawarar ziri daya da hanya daya, ta samar da wata babbar kasuwa ga fina-finan kasar Sin a kasashen ketare, ta yadda idan aka ci gaba da cimma burin yada al'adun fina-finai a ketare, hakan zai kara karfafa zumuncin dake tsakanin al'ummomin kasashen da suka shiga shawarar ziri daya da hanya daya, tare kuma da ingiza hadin gwiwar cinikayyar dake tsakaninsu a nan gaba.

Ana sa ran cewa, shawarar ziri daya da hanya daya, wadda take hada cinikayya a kasa, da kuma kan ruwan teku, za ta tsara wani sabon tsarin cudanyar al'adun dake tsakanin kasa da kasa, bikin nunin fina-finan kasa da kasa na Beijing wanda ake shiryawa sau daya a kowace shekara, wanda shi ma zai ci gaba da himmantu domin samar da wani dandali mai inganci, bisa tushen yin hakuri da juna ga masu aikin samar da fina-finai na kasa da kasa, ta yadda za su taru wuri daya su yi cudanyar al'adu, tare kuma da samun moriyar juna.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China