in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shawarar 'Ziri daya da hanya daya' ta hade burin kasar Sin da na duniya
2017-12-29 14:00:25 cri

A shekarar 2017, 'Ziri daya da hanya daya' ta kasance kalmar da kullum ake amfani da ita a dandalin diplomasiyyar kasa da kasa. A wannan shekara, an cimma nasarar shirya taron koli na dandalin tattaunawar hadin kan kasa da kasa game da shawarar 'Ziri daya da hanya daya' karo na farko a nan birnin Beijing. A wannan shekara kuma, an shigar da shawarar 'Ziri daya da hanya daya' a cikin kudurin kwamitin sulhun MDD. Kana a dai shekarar, an soma gina wasu muhimman ayyukan da suka shafi shawarar cikin sauri.

Yanzu ga karin bayani da wakiliyarmu Bilkisu ta hada mana.

Nan da shekaru hudu kacal da kasar Sin ta gabatar da shawarar 'Ziri daya da hanya daya', shawarar ta riga ta samu karbuwa da jawo hankulan kasashe da yawa, kasashe da yawa sun cimma ra'ayin bai daya a kai, yanzu haka shawarar ta kasance dandalin hadin kan kasa da kasa mafi samun makoma mai kyau a duniya.

"Yanzu haka, ina sanar da cewa, an bude taron kolin na tattaunawar hadin kan kasa da kasa game da Ziri daya da hanya daya."

A watan Mayun na shekarar bana, an shirya taron koli na dandalin tattaunawar hadin kan kasa da kasa game da shawarar "Ziri daya da hanya daya" a nan birnin Beijing, wanda ya kawo halartar wakilai kimanin 1500 da suka fito daga kasashe sama da 130 da kungiyoyin kasa da kasa sama da 70, ciki har da wasu shugabanni 29 na kasashe da gwamnatoci, inda suka tattauna babban shirin hadin kai tare da kasar Sin.

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyanawa baki yanayin da ake ciki na gabatar da shawarar "Ziri daya da hanya daya".

"Bisa yanayin da ake ciki na dogaro da juna tsakanin kasashe daban daban, da bullar kalubale daban daban da duk duniya ke fuskanta, da kyar ake iya kawar da matsaloli bisa karfin wata kasa guda, kuma haka nan ba a iya warware matsalolin da duniya ke fuskanta. Sai dai fa idan an hada kan manufofin kasa da kasa, da kara hada kan albarkatun tattalin arziki da na ci gaba a duk fadin duniya, da haka ne kuma za a iya inganta zaman lafiya, da ci gaban duniya tare."

Tun bayan da shugaba Xi Jinping ya gabatar da shawarar "Ziri daya da hanya daya" a shekarar 2013, kullum kasar na bin manufar yin shawarwari da cimma moriya tare, tana kuma maraba da hadin kai tare da kasashe daban daban na duniya. A cikin shekaru hudu kacal, an mayar da shawarar daga fata zuwa aiki na zahiri. A matsayinsa na mai gabatar da shawarar, sau da yawa Xi Jinping ya bayyana cewa, ko da yake kasar Sin ce ta gabatar da shawarar, amma kasashen duniya ne za su ci moriya daga gare ta.

"Ana gudanar da shawarar 'Ziri daya da hanya daya' ba domin musunta sauran manufofi ba, dai domin tabbatar da hadin kan manyan tsare-tsare da neman bukatar juna wajen fifiko. Ko kasashen Asiya da Turai, ko kuma na Afirka da Amurka, dukkansu abokan hadin kai ne na gudanar da shawarwar 'Ziri daya da hanya daya'. Za a tattauna kan shawarwari tare, kuma za a mori nasarar da aka cimma tare."

Idan an duba ayyukan diplomasiyya da shugabannin kasar Sin suka yi a cikin shekarar nan, ana iya gano cewa, shawarar "Ziri daya da hanya daya" ta kasance wani batun da ya fi muhimmanci na harkokin diplomasiyyar kasar Sin, kuma ta kasance muhimmin batu da shugabannin kasashen ketare su kan ambata.

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya ce:

"Mun yi imanin cewa, za a iya yin kwazo wajen inganta bunkasuwar dunkulewar Turai da Asiya wuri daya a nan gaba, bisa kokarin da ake yi na kawancen tattalin arzikin Turai da Asiya, da shawarar 'Ziri daya da hanya daya', da kuma kungiyar hadin kai ta Shanghai ta SCO. Muna mai da muhimmanci kwarai kan shawarar 'Ziri daya da hanya daya', da kuma hakikanin matakai da za a tabbatar. Muna sa ran alheri ga makoma a nan gaba, tare kuma da fatan kafa dangantakar abokantaka tare da bangarori daban daban a dukkan fannoni."

A shekarar bana kuma, akwai wasu muhimman ayyuka biyu na raya shawarar "Ziri daya da hanya daya". Wato a watan Maris, kwamitin sulhun MDD ya zartas da kuduri mai lamba 2344, inda a karon farko aka shigar da samar da al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil' adama a cikin kudurin, aka kuma yi kira ga kasashen duniya da su karfafa hadin kai a shiyya-shiyya ta hanyar raya shawarar "Ziri daya da hanya daya". Ban da wannan kuma, a watan Oktoba, an shirya babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 19 a nan birnin Beijing, inda aka shigar da shawarar din a cikin tsarin mulkin jam'iyyar.

Shehu malami na jami'ar Renmin ta kasar Sin Wang Yiwei ya ce, wandannan ayyuka biyu sun nuna cewa, shawarar "Ziri daya da hanya daya" babbar manufar kasar Sin ce cikin dogon lokaci, ita ce kuma ta nuna ra'ayin bai daya da kasashen duniya ke fatan cimmawa. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China