Kwamitin sulhun ya sake nuna kulawa ga yanayin jin kai da ya tsananta a kasar Yemen, kana ya yi kira ga bangarori daban daban da su bi dokokin hakkin dan Adam na duniya da dokokin jin kai, da tabbatar da tsaron fararen hula musamman kananan yara. Kana kwamitin ya bukaci bangarorin da su nuna goyon baya ga masu aikin jin kai da kayayyakin jin kai su shiga kasar Yemen cikin tsaro da sauki.
Kwamitin sulhun ya jaddada cewa, warware batun ta hanyar siyasa, ita ce hanya daya kawai ta kawo karshen rikicin kasar Yemen, kuma yarjejeniyar Stockholm muhimmin mataki ne wajen daidaita matsalar. Kwamitin sulhun ya yi kira ga bangarori daban daban da su yi mu'amala da hadin gwiwa tare da manzon musamman na babban sakataren MDD wajen aiwatar da yarjejeniyar yadda ya kamata. Kwamitin sulhun ya jaddada cewa, ana ci gaba da yin kokarin tabbatar da ikon mallaka da 'yancin kai da dinkuwar dukkan kasa da cikkaken yankin kasar Yemen. (Zainab)