A cewar mazauna yankin, an kaddamar da haren haren ta sama ne da rana tsaka, inda aka yi kokarin afkawa wata masana'antar hada karafu dake kusa da wata makaranta a yankin Sawan da ke gabashin birnin Sanaa.
Yousif al-Hadri, kakakin ma'aikatar lafiya a yankin dake hannun 'yan tawayen yace, adadin mutanen da suka mutu ya karu daga mutum 5 zuwa 11, "yawancinsu mata ne 'yan makaranta," wadanda aka raunata kuma ya karu zuwa 39, wanda har ya shafi wasu mutanen dake wucewa ta yankin.
Kakakin ya bayyana cewa, an shirya kai harin ne kan makaranta. An hana 'yan jaridu damar shiga inda lamarin ya faru tun bayan kaddamar da hare haren ta sama.