Mr Heitz ya bayyana cewa, bisa binciken da aka yi a halin yanzu, tsautsayi ne ya haddasa tashin gobara. Abin mai wuya ne a yi binciken, idan aka gama aikin gyara ginin majami'ar, za a kara sauri wajen yin binciken.
An ce, 'yan sanda 40 da jami'an hukumomin shari'a fiye da 10 sun fara yin binciken, wadanda suka bada tambayoyi ga mutanen da suke gyara majami'ar kafin tashin gobarar. Bisa labarin da mutane masu kallon batun suka bayar, watakila gobarar ta fara tashi ne daga karkashin hasummiyar majami'ar dake dab da gabar kogin Seine.
Gobara ta tashi a majami'ar Notre Dame a ranar 15 ga wannan wata, inda ta lalata rufin dakin da hasummiyar majami'ar, amma an kiyaye babban ginin majami'ar. (Zainab)