in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kashe gobarar da ta tashi a majami'ar Notre-Dame
2019-04-16 19:48:59 cri
Rahotanni daga birnin Paris na kasar Faransa na cewa, yanzu haka an yi nasarar kashe mummunan gobarar nan da ta tashi a majami'ar Notre-Dame dake tsakiyar birnin Paris, bayan da ta shafe kusan sa'o'i 15 tana ci.

Hukumar kashe gobara ta birnin Paris ta wallafa a shafinta na Twitter cewa, kimanin 'yan kwana-kwana 400 ne suka garzaya wurin da lamarin ya faru, yayin da 'yan sanda biyu da ma'aikatacin kashe gobara daya suka ji rauni. Hukumar ta ce, wutar ba ta lalata ginin majami'ar da ragowar zanen dake jikinta ba.

Masu shigar da kara na birnin Paris sun bayyana cewa, 'yan sanda za su gudanar da bincike, don gano musababbin tashin gobarar, da ake ganin daga indallahi ne

Ana daukar majami'ar Notre-Dame, a matsayin daya daga cikin misalai masu kayatarwa na tsarin gine-ginen Gothic na Faransa, wadda kimanin mutane miliyan 12 ke ziyarta a kowace shekara.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China