Cikin wani gajeren sakon talabijin da ya gabatar ga al'ummar kasar, shugaban Macron ya ce "Za mu sake gina Notre Dame, ta yadda majami'ar za ta fi da kayatarwa, ina kuma son ganin an kammala aikin cikin shekaru 5 ".
Da yammacin ranar Litinin ne dai gobara ta lakume ginin majami'ar. Wasu hotunan da aka yada ta kafafen yanar gizo sun nuna yadda hayaki ya turnuke rufin hasumiyar majami'ar, yayin da wuta ke cin sassan ginin dake tsakanin manyan kararawa biyu dake saman ta.
Duk dai da cewa ba a fayyace kiyasin adadin asarar da aka yi sakamakon gobarar ba, amma tuni sassa daban daban suka yi alkawarin taimakawa da kusan kudi har Euro miliyan 700, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 790, domin sake ginin majami'ar mai tarihin shekaru kusan 850.(Saminu Alhassan)