Jaridar ta ce layin dogon zai fara aiki ne daga shekarar 2020, zai kuma kasance mai muhimmancin gaske, kasancewar zai hada birnin Beijing, da sabon filin sauka da tashin jiragen sama na birnin, wanda a yanzu ake ginawa.
Bugu da kari, an tsara fara amfani da yankin layin dogon bangaren birnin Beijing, nan da watan Satumbar bana, wanda shi ne zai hade birnin da sabon filin jiragen saman da ake ginawa.
Jiragen kasa da za su rika bin layin dogon dai za su kasance masu gudun kilomita 250 zuwa 350 a dukkanin sa'a guda, za kuma su rage lokacin zirga zirga tsakanin birnin Beijing zuwa Xiongan daga sa'oi 2 zuwa mintuna 30.
An fara amfani da hidimar manhajar taswirar tauraron dan Adam ta BeiDou ne tun daga watan Disambar 2018.(Saminu Alhassan)