Sanarwar da hukumar kididdiga ta kasar Sin ta fitar, ta ce alkaluman GDP na kasar sun kai yuan trillion 21.343, kwatankwacin dala triliyan 3.18 a cikin watanni 3 na farkon shekarar nan, sannan yanayin tafiyarsa daya ne da na rubu'in karshe na 2018.
Bangaren ba da hidima shi ne ke ci gaba da samun tagomashi, inda ya karu da kaso 7 zuwa yuan triliyan 12.232, wanda ya kai kaso 57.3 na jimilar alkalumnan GDP, adadin da ya karu da kaso 0.6 a kan na makamancin lokacin a bara.
Ana ci gaba da bukatar kayakin amfanin yau da kullum, inda bangaren ya bada gudunmuwar kaso 65.1 a ci gaban da aka samu rubu'in na farko.
Bangaren masana'antu ya karu da kaso 6.1 yayin da na ayyukan gona ya karu da kaso 2.7. (Fa'iza Mustapha)




