in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamfanin Huawei ya sanya hannu kan kwantiragin kafa fasahar sadarwa ta 5G guda 40
2019-04-17 09:26:31 cri

Ya zuwa ranar 15 ga watan Afirilun nan, babban kamfanin harkokin sadarwa na kasar Sin Huawei, ya sanya hannu kan kwantiragin kafa fasahar sadarwa ta yanar gizo ta 5G har guda 40. Hakan a cewar mahukuntan kamfanin wani mataki ne na shigar kamfanin karin harkokin cinikayya.

Mataimakin shugaban kamfanin Ken Hu, shi ne ya bayyana hakan, yayin taron kamfanin na bana game da binciken ayyukan sa, wanda ya gudana a hedkwatar kamfanin dake birnin Shenzhen dake kudancin kasar Sin.

Mr. Ken ya ce kamfanin Huawei ya yi hasashen cewa, yawan mutanen dake amfani da fasahar yanar gizo ta 5G na iya kaiwa mutum biliyan 2.8 nan da shekarar 2025.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China