in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin: an kwace hauren giwa da kayayyakin hauren giwa fiye da ton 8 da aka yi fasa kwauri a bana
2019-04-15 13:43:33 cri

A shekarar da muke ciki, sassan yaki da fasa kwauri na hukumomin kwastam na kasar Sin sun bi bahasin laifuka guda 182 wadanda suka shafi halittun da ke dab da karewa da kuma yin fasa kwaurin kayayyakin da aka kera da su, ciki had da wasu guda 53 da ke shafar hauren giwa, tare da kwace kayayyakin hauren giwa ton 8.48 baki daya.

A cikin mummunan laifukan fasa kwaurin hauren giwa da aka gano a ranar 30 ga watan Maris, an kwace hauren giwa fiye da ton 7, tare da murkushe wata kungiyar aikata laifi ta kasa da kasa baki daya, wadda ta dade tana fasa kwaurin hauren giwa.

Har ila yau kuma, kasar Sin tana daukar tsauraran matakai kan yaki da yin fasa kwauri da sayar da hauren giwa da sauran halittun da ke dab da karewa da kayayyakinsu kan yanar gizo ta Internet. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China