in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
WIPO: kyawawan fasahohin Sin na kiyaye ikon mallakar fasaha sun dace a yi koyi da su
2019-04-15 13:26:22 cri

Za a yi taron koli na dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa kan raya shawarar "ziri daya da hanya daya" karo na 2 a karshen watan Afrilun bana a nan Beijing. Francis Gurry, babban sakataren kungiyar harkokin ikon mallakar fasaha ta kasa da kasa wato WIPO, wanda zai halarci taron a Beijing ya bayyana wa manema labaru a kwanakin baya a Geneva cewa, kasar Sin ta tanadi dabaru kiyaye ikon mallakar fasaha cikin manyan tsare-tsarenta, kuma tana mai da hankali kan kiyaye ikon mallaka fasaha a mabambantan sassan tattalin arziki. Kana kuma ya yaba wa aniyar da kasar Sin take nunawa game da tsayawa kan bin manufar kiyaye ikon mallakar fasaha, inda ya ce ya dace kasashe masu alaka da shawarar "ziri daya da hanya daya" da su yi koyi da su.

Rahoton shekara-shekara da kungiyar WIPO ta kaddamar a bana ya nuna cewa, a shekarar 2018 da ta gabata, kasar Sin ta zama kasa ta biyu da ta fi gabatar da bukatun neman ikon mallakar fasaha a duniya. Kamfanin Huawei na kasar Sin kuma ya zama na farko a cikin kamfanonin kasa da kasa, inda ya gabatar da bukatun neman ikon mallakar fasaha 5405 baki daya a duniya. A cewar mista Gurry wannan shi ne matsayin bajinta da wani kamfani ya kafa a tarihi. Ban da haka kuma, rahoton da kungiyar WIPO da sauran kungiyoyi suka kaddamar dangane da yin kirkire-kirkire a duniya a shekarar 2018 ya nuna cewa, a karo na farko, kasar Sin ta shiga jerin kasashe guda 20 mafiya karfin yin kirkire-kirkire a duniya, inda ta kai matsayi na 17. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China